Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da naɗin sabbin Sakatarorin din-din-din a ma’aikatun gwamnatin tarayyaCikin farkon Makon nan ne a kasarmu rahotannin kan tafiyar Mai girma shugaban kasa Nijeriya Muhammadu Buhari ƴan kwanaki kaɗan bayan tafiyar sa sanarwa dake cewa ya amince da nadin sababbin sakatarorin din-din-din a ma’aikatun gwamnatin tarayya ta fito.

Wannan sanarwa ta zo ne cikin wani jawabi da shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya, tayi Dr. Folashade Yemi-Esan ta fitar da wannan sanarwa a babban birnin tarayyar Nijeriya a Abuja.

Jaridar The Nation ta wallafa wannan rahoto cewa Dr. Folashade Yemi-Esan ta bayyana cewa za a maye guraben wasu sakatarorin da su ka bar aiki karkashin gwamnatin tarayya cikin shekarar data gabata 
Yemi-Esan ta ce yawancin sakatarorin din-din-din da su ka yi ritaya a shekarar nan sun fito ne daga jihohin Ekiti, Enugu, Katsina, Legas da Nasarawa.

Shugaban Muhammadu Buhari ya bada dama a fara shirye-shiryen zakulo wasu sababbin sakatarorin ne tun kafin tafiyar sa ƙasar waje.

Hakazalika Shugaban ma’aikatan gwamnatin Najeriya ta ce za a cike guraben ne da jami’an gwamnatin da su ka kai matsayin darekta a mataki na 17 a 2019.

Ma’aikacin gwamnatin tarayya da ya zama darekta a ranar 1 ga watan Junairu, shekarar 2019 ko kafin nan ne kadai za ayi la’akari da shi wajen zabin matsayin sakataren a cewar ta.

Yemi-Esan ta bukaci sakataron din-din-din masu-ci, su aiko mata da sunayen darektocin da su ke kan matakin aiki na 17 a ma’aikatunsa dake faɗin ƙasar

An umarci sakataron su aiko da duk wasu bayanan waɗannan ma’aikata da kuma takardu na 20 na neman aikinsu watau Curriculum Domin tantance su

A cikin farkon makon nan kun ji cewa mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari kan ya fita ya yi naɗa-naɗen sababbin darektoci a Ma’aikatar NASENI.

Dr. Olayinka Adunni Komolafe ta zama sabuwar Darektar hukumar NASENI. Ana sa ran ita da sauran darektocin hudu za su sauka a 2026 mai zuwa.