Ƙungiyan NURTW zata biya Miliyan goma sha ɗaya da dubu ɗari biyar ga ƙungiyar NATO a Keffi.Tsawon lokacin da aka kwashe wajen sauraron hukuncin da Kotu zata yanke game da shari'ar dake tsakanin ƙungiyar direbobi na NARTO Da kuma NURTW rashen karamar hukumar Keffi dake jihar Nasarawa.

Yau Talata 30-3-2021 kutun ta yanke hukuncin kan laifuffukan da suka gabata kimanin guda goma tunda ga korafi kan lalata wa Narton motoci takardun ruwaito na booking pass tsabar kudi da dai sauran su bayan kammala karanto bayanan da suka gabata mai shari'ar ya bayyana gamsuwa kotun da shaidu da hujjojin da Lauya mai wakiltar NARTO yaya gabatarwa tsawon shekaru.


A karshe ya yanke wa NURTW hukuncin biyan zunzurutun kuɗaɗe Kimanin Naira miliyan goma sha daya da dubu ɗari biyar

Barista Mustafha Bashir ya bayyana wannan gagarumin nasara da cewa Narton ce kaɗai tayi ba nasarace ta al'umma baki daya wanda ke nuna cewa an waye kuma an fahimci doka har ta kai ga al'umma ba sa ɗaukar doka da hannun su.

Hakazalika yayi kira ga ƙungiyoyin biyu da su yi amfani da wannan gagarumin Nasara matsayin hanyar da zata magance rikicin dake tsakanin kungiyoyin Kasancewa wannan sana'a da suke yi hanya ce ta neman abincin su na Yau da kullum.

Maiwada sidi shugaban NARTON ya bayyana godiyar sa ga Allah ga da wannan gagarumar nasara kana ya yabawa Alkali da  lauyan sa game da jajircewar su a kan gaskiya

Mun yi kokarin jin ta bakin lauyan waɗanda ake ƙara Wato NURTW amma abin ya ci tura da zarar mun samu tattaunawa da ɗaya bangaren zamu cigaba da ruwaito muku rahoton

Abas Aliyu Rizy