Ƙungiyar Real Madrid zata cefano mai tsaron gida De Gea Daga Manchester


Ƙungiyoyi biyu na ƙasar Ingila Manchester United da Manchester City sun nuna sha'awarsu ta sayen ɗan wasan Villarreal Pau Torres mai shekara 24. 

Ƙungiyar Manchester United za ta saurari tayin sayen mai tsaron raga David de Gea mai shekara 30 a kakar wasan nan inda kocin ƙungiyar Ole Gunnar Solskjaer ya ce a shirye yake ya mayar da Dean Henderson na ɗaya.


Rahotanni su sanar da cewa ƙungiyar Arsenal a shirye take ta yi amfani da dambarwar da ke faruwa a Inter Milan wajen gabatar da buƙatarta ta neman ɗan wasan baya na Morocco mai shekara Achraf Hakimi.