Search Items

Ƙungiyoyin na rububin ɗan wasa Sergio Aguero ɗan ƙasar ArgentinaDan wasan baya na Faransa Malang Sarr, mai shekara 22, zai koma ƙungiyar Chelsea a karshen zamansa na aro da yake a Porto a karshen kakar bana.

Ƙungiyar Arsenal ta zama kungiya ta baya bayan nan da ke sha'awar daukar dan wasan gaba na Fiorentina Dusan Vlahovic, mai shekara 21, inda ta biyo sahun su Tottenham, da AC Milan, da RB Leipzig da Roma da kuma Atletico Madrid wajen neman dan kasar ta Serbia.Kocin Paris St-Germain Mauricio Pochettino da darektan wasanni na kungiyar Leonardo na aiki ba kakkautawa domin ganin sun dauki Sergio Aguero mai shekara 32 dan wasan gaba na Argentina, da zai bar Manchester City da zaran wa'adinsa ya kare a karshen bazara.

Sai dai kuma alamomi na nuna Barcelona, ce za ta yi nasara wajen dauke dan wasan da ya dauki kofin Premier hudu, wanda kuma ake cewa Real Madrid da Juventus ma na harinsa (Manchester Evening News)Ƙungiyar Manchester United, da Liverpool da kuma Tottenham na fafutukar sayen dan wasan tsakiya na Austria Marcel Sabitzer, mai shekara 27, daga ƙungiyar RB Leipzig a karshen kwari dangin sa.

A shirye ƙungiyar Everton ta ke ta saurari tayi daga duk wata ƙungiya da ke son sayen ɗan wasan bayanta Yerry Mina. Za ta sayar da ɗan wasan ne ɗan ƙasar Colombia mai shekara 26 domin samun kuɗin da za ta sayi dan wasan baya na Napoli Kalidou Koulibaly, ɗan Senegal mai shekara 29. (Football Insider)

Manchester City ta ƙaryata cewa tana da niyyar daukar ɗan wasan bayan Bayern Munich David Alaba, duk da rade-radin da ake yaɗawa cewa za ta ɗauki ɗan wasan mai shekara 28, wanda zai bar zakarun na Jamus a lokacin bazara. (Manchester Evening News)

BBC Hausa