Search Items

"Da Walaki Goron a Miya" Gudanar da bukin zagayowar shekarun haihuwar Ahmad Bila Tunibu a kano


Masana harkokin siyasa a Najeriya sun fara tsokaci kan bikin zagayowar ranar haihuwar Sanata Ahmad Bola Tinubu, jigo a jam'iyyar APC mai mulki da ake yi a Jihar Kanon dake arewacin Najeriya.

Wannan shine karon farko da ake yin bikin zagayowar ranar haihuwar nasa  a wata jiha da ke arewacin Najeriyar, inda a baya an fi yin bikin a mahaifar Tinubu wato Legas.

Gabanin taron, Tinubu ya kai ziyara tare da duba wasu daga cikin ayyukan da gwamnatin Kano ta yi a jihar sannan ya gana da ƙabilun yankin kudancin kasar mazauna Kano da kuma wasu daga cikin malaman addinin Musulunci a jihar.

Ko Kafin zuwan Ahmad Tinubu Kano,  ya je Jihar Katsina a makon da ya gabata, har ma ya bai wa 'ƴan kasuwar da gobarar babbar kasuwar jihar ta shafa tallafin kuɗaɗen.

A yanzu haka dai manyan ƴan siyasa daga jam'iyyar APC da masu riƙe da muƙamai daga sassan ƙasar nan daban-daban su ka je Kano don halartar wannan gagarumin bikin na ranar zagayowar haihuwar jigon

Sai dai mai bai wa Shugaba Muhammadu Buhari shawara kan harkokin siyasa, Sanata Babafemi Ojudu, ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa rashin kyawun yanayi ya hana wasu manyan ƙasar da dama tafiya Kanon ɗan halartar bikin.

Ya ce: "Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Asinbajo, da Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha, da Kakakin Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila da ni kaina ba za mu samu damar halartar taron ba, sakamakon rashin kyawun yanayi da ake fama da shi a Kanon, dalilin da ya hana tashi da saukar jiragen sama."

Malam Kabiru Sufi, masanin kimiyyar siyasa ne a kwalejin share fagen shiga jami'a ta CAS a Kano, yana da ra'ayin cewa lallai da walakin goro a miya.

Gabatar da wannan taron a Kano ba haka kawai bane akwai alamar cewa Tunibu ya fara nuna aniyar sa ta siyasa ga yan arewacin Najeriya

Source BBC Hausa