Yau 11 ga watan Maris ce Ranar ƙoda ta Duniya

Yau ce ranar ta musamman wanda hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta amince da shi a matsayin Ranar ƙoda

Dr Aisha Nalado, wata likitar ƙoda da ke aiki a asibitin koyarwa na qMallam Aminu Kano da ke jihar Kano cikin hirar ta da wakilin BBC ta bayyana cewa "a cikin kashi 100 za a ce kashi 20 na mutane suna ɗauke da cutar ƙoda".

Ta bayyana cewa cutar ta ƙoda tana iya kama kowa daga manya har ƙanana - a kowane lokaci na rayuwa za a iya samun cutar ƙoda.

Ƙwararru sun bayyana cewa ana iya gujewa kamuwa da cutar ƙoda ta hanyar rage shan sigari, magunguna masu rage raɗaɗin cewa da sauransu.