Search Items

Yunƙurin juyin mulki tasa wani Hafsan sojin kasar Nijar tserewa daga ƙasarSojan da ake zargin sa da jagorantar yunƙurin juyin mulki a Jamhuriyar Nijar a daren Laraba ya tsere, a cewar kafofin yaɗa labaran Faransa a cewar bayanan farko-farko, wani sojan sama mai suna Kaftin Gourouza, shi ne shugaban maharan da suka isa a motoci guda huɗu a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP yana mai ambato gidan rediyon RFI.

Shugaban nasu wanda yanzu haka ake nemansa ruwa a jallo, ya tsere, a cewar majiyoyin tsaro ta ƙasar

Hakazalika Wata majiyar tsaro ta shaida wa AFP cewa an kama wasu sojoji guda  biyu bayan yunƙurin juyin mulkin.Gwamnatin kasar ta tabbatar da yunƙurin juyin mulkin yayin da aka sanya birnin Yamai a cikin shirin ko-ta-kwana.

Tun misalin ƙarfe 3:00 na tsadar dare aka fara jin harbe-harbe a kusa da Fadar Shugaban Ƙasa kuma an ɗauki kusan minti 15 ana yi.

Jami'an tsaron fadar ne suka daƙile yunƙurin, wanda ya faru ƙasa da kwana biyu kafin rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Mohamed Bazoum.

BBC ta tuntubi Dakta Gambo Alhaji Sani, wani masanin siyasa a Zinder don jin yadda yake kallon wannan harbe-harben da aka yi da wasu ke zargin ko yunkurin juyin-mulki ne a kasar.

Ya ce "kawo yanzu hukumomi ba su yi bayani a hukance kana bin da ya faru ba, amma wasu na ganin wata makarkashiya ce ta hana zanga-zangar da aka shirya yi a ranar Laraba.

''Amma idan ya kasance cewa da gaske yunkurin juyin mulki ne, to tabbas dimokradiyyarmu gurguwa ce.

"Ya nuna ba a mutunta doka, da ta ce a bai wa al'umma abin da suka zaba na shugaban kasa, sannan mafarkin da ake yi na cewa juyin-mulki ya zama tarihi a jamhuriyar Nijar ya kau ba.''

Ya kara da cewa ba a san al'ummar Nijar ko 'yan siyasa da tashin hankalin bayan zabe ba, yawanci da zarar an sanar da sakamakon zaben wanda ya sha kaye na kiran dan uwansa ya masa murna da fatan alkhairi.

Sai dai a wannan karon hakan bai samu ba, duba da yadda aka shirya zaben.

''Tun da aka kada gangar siyasa shekara biyu da suka wuce ake zaman doya da manja tsakanin 'yan hamayya da 'yan mulki, kan tababa akan takarar madugun adawa Hama Amadu da Bazoum Muhammad da kotu ta sanar ya yi nasara.

''Aka zo aka dora hukumar zaben da dukkan bangarorin ba su aminta da ita ba, Kotun Ƙoli ma wani bangare bai amince da shi ba. Wannan na daga cikin abin da ya kara rura rikici tsakanin bangarorin biyu.''

Ya ce mafita a nan ita ce a mutunta doka, muddin masu mulki da 'yan adawa ba za su mutunta dokokin dimokradiyya ba tabbas za a ci gaba da ganin irin wannan matsala.