Search Items

Zai yi wuya a tsallake karin farashin Man fetur a Najeriya


Masana harkokin tattalin arziki da cinikayya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu dangane da furucin da Shugaban Kamfanin Mai na Najeriya, Mele Kyari, ya yi cewa gwamnati na kashe makudan kuɗaɗe wuri na gugar wuri har naira biliyan 120 a kowane wata a matsayin tallafin man fetur ga masu sana'ar fetur Najeriya.

Mele Kyari wanda ya bayyana hakan ya ce kamfanin ba zai iya ci gaba da biyan waɗan nan makudan kuɗaɗe ba, saboda haka dole ne 'yan Najeriya su hakura su sayi man fetur bisa yadda farashin ya kama komai tsadar sa.

Dr Ahmed Adamu, wani masanin ne  kan tattalin arziki da ya shafi man fetur a jami`ar Nile da ke Abuja ya shaida wa BBC cewa zai yi wuya gwamnatin ta dore da biyan makudan kuɗaɗe a matsayin tallafin mai saboda irin ɗawainiyar da ke kanta da kuma yadda bukatar mai ke kara karuwa a kasar.

A cewar Dr Ahmad, gwamnati ta yi gaggawar cire tallafin mai ba tare da duba abubuwan da suke faruwa ba. Ya ce tallafin man fetur abu ne da ya zama dole a Najeriya saboda akwai matakan da ya kamata a ce sai an samar da su sannan a cire tallafin.

Masanin tattalin arzikin da ya shafi man fetur ya ce abu ne mai wuya ba a samu karin farashin mai ba a kasar "duk da cewa ya danganta da wasu abubuwa".

Ya ce lamarin ya danganta da farashin man fetur ɗin a kasuwar duniya, "idan farashin ɗanyen man fetur ya ci gaba da hauhawa kamar yadda yake a baya-bayan nan, kudin da ake shigo da tataccen mai zai kara tsada kuma idan ya kara tsada nauyin tallafin da gwamnati ke badawa zai yi mata yawa har lokacin da za ta ce ta gaza toh yan Najeriya dole su sayi mai da tsada".

A cewarsa, idan kuma aka samu farashin danyen mai a duniya ya yi kasa, toh kudin da ake shigo da tataccen mai zai ragu.

BBC Hausa