Akwai yiwuwar samun durƙushewar aikin noma a arewacin Najeriya sakamakon rashin tsaro


Masu hasashen al'amurra da nazarin rayuwa na hangen za'a samu matsalar wadataccen abinci da ga manoma a arewa maso yammacin Najeriya sakamakon illan da ƴan bindiga suka yi wa mazaunan karkara musamman manoma wanda rashin zaman lafiya ya sa suka yi gudun hijira.

Rashin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali musamman a jihohin arewa maso yammacin Najeriya ya sa har yanzu manoman da suka yi gudun hijira ba su koma ga gonakinsu ba, matakin da ya rage yawan abincin da ake samarwa a ƙasar.

Wani manomi Isah Musa da ya yi gudun hijira daga ƙauyen Jangebe zuwa garin Gusau a jihar Zamfara ya ce kafin ya yi gudun hijira yana noma sosai wanda yake ci da iyalinsa har ya kai kasuwa ya sayar amma yanzu ba ya da halin yin noman.

"Ɓarayi suka addabe su suka gudu, yanzu ba wani aikin da yake sai lebaranci," in ji shi.

Irin wannan al'amari na kauracewa matsuguni a gurin mutanen karkara musamman wadanda suke yankin Zamfara da makwabtan su ya haifar da ƙarancin Manoma dake Samar da abinci da yawa a arewacin Najeriya.