Ƴan Arewa kaɗai ke bada wuta da aljanna: cewar Alaramma Salisu MuhammadA Najeriya ne kaɗai ake yanke wa mutane hukuncin aiyukan su ƴan wutane ko ƴan aljanna tun suna raye basu mutu ba musamman a ɓangaren bahaushe dake arewacin Nigeriya.

Wannn kalami ya fito ne daga baki Alaramma Salisu biyo bayan suka da zargi da wani matashin arewa yayi ta caccakar Jarumar fim Rahama Sadau bayan raba kayan abinci da tayi ga ma'aikata cikin wannan wata na Ramadan.

Cikin kalaman matashin ya bayyana cewa babu kishin musulunci ko kishin arewa cikin tsarin ta don haka aikin banza ta keyi don hakama ba abin a yaba mata bane.

Alaramma Salisu ya bayyana wannan kalamai da sunan cin mutunci ko kuma kunshe da hassada ga Jarumar.

Hakazalika ya ce wannan ba shine irin sa na farko ba a kwanakin baya an samu wata Jarumar fim ta gina masallaci amma sai gashi matasa na ta suka da caccakar wanna kokari da tayi maimakon Inma ba za'a yaba ba to aiyi shirin.

Kamar yadda addinin Musulunci ya tanada cewa ka faɗi alkhairi ko kayi shiru.

Cikin jawabin sa yace tsakanin bawa da ubangiji sai shi ba karamin kuskure bane mutun yayi aikin sa na alkhairi wani ya duɓe shi yace Allah bai karɓa ba. kana bashi da wata hujja da zai iya bayarwa a addinance sai dai kawai abin da yayi daidai da ra'ayin sa.

A karshe malamin yayi kira ga al'ummar Musulmi da su dubi girman wannan wata mai albarka su kyautata aiyukansu don samun cikakkun sakamako daga Allah.

Shuraih Usman