Ƴan Banga sun yi nasarar kashe Ƴan bindiga 10 a daren jiya juma'a a kauyen ƙwaya ta jihar Zamfara


Rahotannin daga jihar Zamfara a arewacin Najeriya na nuna  cewa wasu ƴan fashin daji sun kwashi kashinsu a hannu a daren Juma'a yayin da suke ƙoƙarin kai  farmaki kan wasu ƙauyuka guda  biyu da ke kusa da babban birnin jihar Zamfara

Ƴan fashin a kalla  mutum10 ne suka mutu a cikin bata kashin da suka yi da ƴan banga a ƙauyukan Kwaya da kuma Kura da ke ƙaramar hukumar Gusau ta jihar Zamfara.

Hakan ya faru ne yayin da mazauna ƙauyukan nan shida da suka kai wa farmaki a shekaran jiya ke cewa adadin wadanda suka mutu a harin daren Laraba  yanzu haka ya kai 80.

A cewar mazauna yankin. ƴan fashin dajin sun gamu da gamon nasu ne a wani karanbatta da suka yi da ƴanan banga a ƙauyukan Kwaya da kuma Kura lokacin da suka yi yunkuri afka musu da tsakar daren jiya.

Wani ɗan sa kai da aka yi fafatawar da shi, ya bayyana wa gidan rediyon BBC Hausa cewa turjiyar da suka nuna da kuma ɗaukin da aka kai daga maƙwabtan ƙauyuka ne suka taimaka musu suka fatattaki maharan tare da hallaka 10 daga cikinsu.

Hakazalika ya tabbatar da cewa "Jiya da misalin sha biyu  da ƴan mintina na dare, da yake ba barci muke ba muna gadi saboda halin da muke ciki. Sai ƴan wancan garin suka kira mu suka ce mukai musu ɗauki ga ƴan fashin sun zomusu.

"Da haka muka je dauke da bindigoginmu na toka duk da cewa su suna dauke ne da AK47 amma a haka muka ci galaba a kansu har muka kashe mutum 10.

"Da suka ga haka sai suka gudu, ba su samu nasarar shiga garuruwan ba. Ko kaza ba su ɗauka, ba a garuruwan Kamar yadda rahoton ya bayyana.