Ɗan bindiga yayi tuban muzuru a jihar Katsina, Auwalu DaudawaDaya daga cikin Shahrarrun ƴan bindigan da suka adabi arewacin Najeriya wanda ya jagoranci satan daliban Kankara 300, Auwalu Daudawa, ya koma daji bayan watanni uku da furta tubarsa daga barandancin da satar mutane.

A cewar jaridar Daily Trust, wata majiyar jami'an tsaro da wasu majiyoyi na kusa da dan bindigan sun tabbatar da cewa Auwalu Daudawa ya koma dajin dake da iyaka da jihar Katsina.

Auwalu Daudawa ne ya jagoranci satan daliban makarantar GSS Kankara ranar 12 ga Disamba, 2020 shekarar da ta gabata.

Hakazalika bayan watanni biyu, gwamnan jihar Zamfara ya sanar da cewa Daudawa ya tuba daga ɗabi'ar garkuwa da mutane kuma ya ajiye makamansa.

Daudawa da yaransa biyar sun mika bindigogin AK47 guda 20, harsasai barkatai, da roka 1.

Majiyoyin sun bayyana cewa Daudawa ya kwashe yaransa sun koma dajin Jaja, dake karamar hukumar Zurmi ranar Litinin.

Bayan tarewar sa  a dajin ne ya kira wani abokin sa yayin da yake sanar da shi cewa ya koma daji.

Ko Kafin hakan sati guda da miƙa makaman sa gwamnati ta saya masa gida kuma ta ci gaba da ɗaukan nauyin sa amma duk da hakkan ya bayyana cewa ba'a cika masa alƙawarin da aka yi masa ba.