An yi ƙarin gishiri kan taron da ake cewa an yi 2021 kan Yakowa cewar Reverend Hayab
Shugaban kiristoci na Najeriya CAN reshen jihar Kaduna Reverend John Hayab ya nuna an yi karin gishiri kan wani taro da a ke cewa an yi a Bauchi a 2010 karkashin jama'atu nasril islam da wai a ka shirya hallaka tsohon gwamnan Kaduna Ibrahim Yakowa.

Hayab ya ce takardar bayan taron da ta ke yawo tun 2010 kuma ta ke nuna ministan sadarwa Dr.Isa Pantami ya jagoranci taron, an yi karin gishiri.

Shugaban na mabiya addinin kirista a Kaduna na magana ne da gidan jaridar yanar gizo na Premium Times.

Hayab wanda ya rike mukamin mai taimakawa gwamna Yakowa kan lamuran addini, ya ce ya na kusa da marigayin kuma ba haka lamarin da a ka yaɗa a takardar ya ke ba.

Malamin na kirista ya buƙaci jami'an tsaro su yi hamzarin ɗaukar mataki kan wannan batu don hana tada fitina.

Hayab ya ce a yi sauri a yaiyafawa wannan fitina ruwa domin fuskantar kalubale da ake fama da su na Yau da kullum.

In za a tuna Gwamna Yakowa ya riga mu gidan gaskiya a hatsarin jirgi mai saukar angulu a jihar Bayelsa tare da tsohon mai ba da shawara kan tsaro Andrew Azazi a 2012.

Yakowa na dawowa ne daga jana'izar mutuwar mahaifin mai taimkawa tsohon shugaba Jonathan , Oranto Doughlas ya riki nasa ajalin.

Hakazalika shugaban ƙasa Muhammadu Buhari Shugaban  ya gana da kungiyar gwamnonin arewa a fadar Aso Rock kan tsaron yankin.

Shugaban ya gana da gwamnonin bisa jagorancin shugaban kungiyar su, gwamna Simon Lalong na jihar Filato.

Ganawar ta ba da dama ga gwamnonin daya bayan daya sun yi bayanin halin da jihohin su ke ciki kan lamuran tsaro da bukatar irin dauki da su ke yi daga gwamnatin taraiya.

Rahoto ya nuna cewa shugaban ya yi alwashin daukar matakin gamawa da miyagun iri da ke addabar yankin arewacin Najeriya kama daga 'yan boko haram, masu satar mutane da sauran 'yan bindiga dadi.


Yahaya Turba