Ƙasar Amurka ta ruwaito Isa Pantami ministan cikin jerin ƴan ta'adda

A yau Litinin  wasu jaridun Najeriya suka wayi gari da wani rahoto da ke ikirarin cewa Amurka ta sanya sunan ministan sadarwa Isa Ali Pantami a cikin jerin sunayen ƴan ta'addan duniya ya ja hankalin ƴan kasar.

Duk da cewa  jaridun da suka wallafa rahoton ba sanannu ba ne, amma batun ya ja hankali sosai musamman a shafin Twitter inda ya kasance ɗaya daga cikin manyan batutuwan da aka fi tattaunawa a kan su a shafin a yau Litinin.

Ratohon ya ambato wasu majiyoyin leken asirin Amurka suna cewa kafin nadinsa a matsayin minista, Isa Ali Pantami yana da tsattsauran ra'ayi game da Amurka sannan ya yi mubaya'a ga kungiyar Al-Qaeda a cewar su.

Kazalika sun ambato wasu bayanai daga abin da suka kira majiyoyin leken asiri na Yammacin Duniya na cewa ministan ya yi alaka ta kut-da-kut da Muhammad Yusuf, shugaban kungiyar Boko Haram na farko kuma yana da dangantaka da Abu Qatada al-Filistini da kuma wasu shugabannin kungiyar Al-Qaeda da suka ce yana matukar girmamawa.

Sai dai har yanzu haka babu wani sahihin rahoto da ke tabbatar da wannan bayani, wasu ƴan Najeriya na da ra'ayin cewa wannan zance ƙazafine kawai yayin da wasu ke ganin cewa kirkirarren Magana ce kawai da Turawan Yamma suka saba yiwa dukkan wani musulmi da suke tunanin ya na da tasiri sosai a cikin al'ummar sa.

Dr Isa Ali Pantami, malamin addinin Musulunci ne da ya yi ta karatutuka a kasashe da dama na duniya ciki har da ƙasar Saudiyya.

Tun bayan ɓullowar ƙungiyar Boko Haram, Pantami yake bayyana ƙyamarsa game da yadda ƙungiyar take gudanar da ayyukanta, lamarin da ya sa ya taɓa yin muƙabala da shugaban ƙungiyar na farko Muhammad Yusuf inda ya ƙalubalance shi kan koyarwar ƙungiyar ya saɓawa karantar wan Manzo Allah.

Irin wannan mataki nasa tasa a shekarar 2020, shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau, ya yi barazanar kashe minista Pantami a wancan lokacin.