Babban kalubalen da ke gaban sabo IG shi ne ya hade kan hukumomin tsaro


Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa DIG Usman Alkali Baba a zaman sabon Mukaddashin Babban Sufeton ƴan sandan Najeriya.

Sabon sufeton ya maye gurbin Mohammed Abubakar Adamu, wanda shekarunsa na ritaya suka cika a farkon wannan shekarar. Ministan harkokin ƴan sanda Maigari Dingyadi ya bayar da sanarwar ranar Talata.

Dama dai tsohon sufeton ƴan sandan Najeriyar Mohammed Adamu ya yi ritaya, amma a ranar 4 ga watan Fabrairun shekarar nan shugaba Buhari ya kara masa wa'adin wata uku, amma watanni biyu kawai ya yi aka nada wani sabon sufeton wanda ya mai gurbin sa.

DIG Usman ya samu mukamin ne a daidai lokacin da Najeriya ke fuskantar kalubalen rashin tsaro a sassa daban-daban na kasar, kama tun  daga satar mutane domin neman kudin fansa, da barayin shanu, da rikici tsakanin manoma da makiyaya da na baya-bayan nan wato hare-hare kan ofisoshin ƴan sanda a yankin kuduncin  ƙasar nan.

Samar da isassun ma'aikata karkashin hukumar ƴan sanda, saboda akwai bangarori da dama a Najeriya da ke aikin ƴan sanda amma kuma aikin ƴanan sanda suke yi.

Misali hukumar kare hadurra ta kasa wato Road Safety, kowa ya san aikin da suke yi ƴan sanda ne ya kamata su yi shi, akwai kuma Civil Defence su ma kamata ya yi a ce suna karkashin ma'aikatar 'ƴan sanda.

Don haka babban kalubalen da ke gabansa shi ne ya hade kan hukumomin tsaro domin aiki tare da samar da tsaron cikin gida yadda ya kamata.

A karshe Kabiru Adamu ya ce matukar aka hada kan jami'an tsaro da dinke barakar da ke tsakaninsu babban makami ne na samar da rundunar tsaro mai karfi.

Amfani da ma'aikatan da ake da su domin cimma tsaron cikin gida da tsare kasa baki daya ƙasa shi ne abin da 'yan Najeriya ke da buri da kuma fatan ganin sabon mukaddashin sufeton 'yan sandan zai yi tsayuwar daka wajen magancewa.

BBC Hausa