Baraka ta Kunno Kai a jam'iyar adawa ta PDP tsakanin ƴaƴanta:kwankwaso da Tambuwal


Da alama wata baraka ta na shirin  kunno kai a reshen jamiyyar PDP na arewa maso yammacin Najeriya, inda daya daga cikin iyayen jam'iyyar a yankin Sanata Rabiu Kwankwaso ya zargi gwamnan Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto  da yin katsalandan cikin al'amuran jam'iyyar a jihar Kano.

A cewar Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso wanda yake jagorantar bangaren Kwankwasiyya ya zargi Tambuwal da haɗa kai da wasu ƴaƴn jam'iyyar na Kano da ke hamayya da shi da mutanensa don taimaka musu su samu shugabancin jam'iyyar na yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

"Abin takaici shi ne akwai shi gwamna na Sokoto, wanda a ra'ayinsa bai kamata mu musamman mu yan Kwankwasiyya a bamu wadan nan mukamai ba". in ji Kwankwaso.

To sai dai a nasa bangaren, gwamna Aminu Tambuwal ya musanta wannan zargin inda ya ce "duk wanda yake da sha'awa ya fito ya yi takatra, ya fito ya yi takara" duk wanda jama'a suka zaɓa shine demokaraɗiya.

Hakazalika Gwamnan Ya kuma nisanta kansa da zargin da Kwankwaso ya yi masa cewa yana da hannu a siyawa Sanata Bello Hayatu Gwarzo fom domin yayi takara.

BBC Hausa