Bukatar shugaba Buhari na dawo da AFRICOM yankin Afirka dai yake da dawo da mulkin mallaka


Tsohon ɗan majalisar dattawan Najeriya Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa ɓukatar da shugaba Buhari yayi na tsarin dawo da hedikwatar rundunar sojoji masu kula da Afirka wato AFRICOM zuwa nahiyar  Afirka daga mazauninta da ke Jamus

Shehu sani ya bayyana hakan a matsayin dawo da tsarin mulkin mallaka Sanata ya bayyana hakan ne bayan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga Amurka ta dawo da rundunar Afirka saboda matsaloli na tsaro.

Gwamnatin ƙasar ta ce kiran wani sauyin matsayi ne ga Najeriya wadda a baya ta riƙa nuna adawa kan yadda ƙasashen yamma ke kafa sansanoninsu a nahiyar Afirka.

Sai dai a yanzu matsalolin tsaron da ake fama da su, sun sanya ganin fa'idar kawo rundunar sojojin ta Amurka yankin Afirka.

Amma wasu ƴan adawa irinsu Shehu Sani sun ce kiran dawo da hedikwatar rundunar Amurkan ba mafita ba ce, don kuwa matakin zai iya buɗe ƙofa ga wani sabon salon mulkin mallaka da kawo sojojin ƙasashen yamma su zo su karkasa ƙasashe ta hanyar rarraba kawunan ƙasashen Afrika.

Source BBC Hausa