Chelsea na shirin cefane ɗan wasan Borussia Dortmund, Erling Braut Haaland,

Ƙungiyar Chelsea na son sayen dan wasan gaba a wannan bazara inda ta fi mayar da hankali a kan tauraron Ɗan wasan Borussia Dortmund, dan kasar Norway Erling Braut Haaland, mai shekara 20, ko kuma Romelu Lukaku, na Inter Milan, dan kasar Belgium mai shekara 27. Cewar Jaridar Sun

Ajax ta ce a shirye take ta sayar da dan bayanta na gefen hagu, dan kasar Argentina Nicolas Tagliafico, mai shekara 28, a kan fam miliyan 13,wanda kungiyoyin Leeds United da Manchester City da kuma Inter Milan dukkaninsu ke sha'awa. (Mail).

Ƙungiyar Manchester United na harin mai tsaron ragar Aston Villa, ɗan Ingila Tom Heaton, mai shekara 35, idan Sam Johnstone, mai shekara 28, shi ma dan Ingila na kungiyar West Brom, ya nun aba ya son komawa kungiyar. 

Jaridar Goal ta ruwaito cewa Darektan wasanni na Paris St-Germain Leonardo ya ce kungiyar ta Faransa ba za ta yi gaggawar kulla sabuwar yarjejeniya ba ta zaman dan wasanta na gaba dan kasar Brazil Neymar, mai shekara 29. 

BBC Hausa