Gwamnatin jihar Nasarawa ta yi Allah wadai da harin taaddancin da aka kai Kauyen AjimakaGwamnan jihar Nasarawa Engr. Abdullahi A. Sule yayi Allah wadai da kakkausar murya sakamakon mummunan kisan gillar da aka yi wa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a karshen makon jiya a Kauyen Ajimaka dake karamar hukumar Doma.

Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana abin da wasu da ba a san ko su waye suka aikata ba da abin zargi, da kuma ƙira da rashin uzuri.

Injiniya. Sule ya bada tabbacin cewa tuni dai jami'an tsaro suka fara aiki binciken domin bankaɗo asirin masu laifin da nufin hukunta su bisa ga dokokin ƙasar

Hakazalika Gwamnan ya miƙa ta'aziyar sa ga Iyalan mamatan da suka rasu tare da tabbatar musu da cewa gwamnati zata yi duk abinda zata iya wajen tabbatar da Adalci,  da zaman lafiya da kuma inganta 
tsaro a fadin jihar.

Gwamnan ya kuma yi kira da a kwantar da hankula tare da tallafawa jami'an tsaro don magance matsalolin da suke addabar jihar Nasarawa da al'ummar ta baki ɗaya.

Wannan sanarwar ta fito ne daga Ibrahim Addra. Babban Sakataren yada labarai na Gwamnatin jihar Nasarawa a ranar 26th Afrilu, 2021

Sadiq Takwar