Hukumar ƙasar Saudiyya ta sanar da cewa an rage yawan Sallah Tarawihi a masallacin Makkah da MadinaJaridar Saudi Gazette ce ruwaito cewa Sarki Salman na Saudiyya ya bayar da umurnin rage raka’o’in sallar taraweeh a Masallacin Harami na Makkah da kuma na Madina.

Jaridar Saudi Gazette ta ce shugaban da ke kula da harakokin Masallatan biyu Sheikh Abdul Rahman Al-Sudais, ya ce za a rage yawan raka’o’in zuwa 10 daga 20 da aka saba yi.

Sannan za a yi Sallar ne bisa bin ka’idojin da aka gindaya na kariya daga yaɗuwar cutar korona.

A ranar Talata Al’ummar Musulmi a faɗin duniya ke fatan soma Azumin watan Ramadan.

A azumin da aka gudanar a bara an dakatar da yin Salloli biyar na farilla da Sallar taraweeh da kuma Umrah.

A bana hukumomin Saudiyya sun amince a gudanar da Umrah, amma an hana yin I’tikaf da kuma buɗa baki a Masallatan biyu.