Jirgin sama samfurin Alpha Jet (NAF475) ya bata a sararin samaniya a Maiduguri


Idan Masu karatu basu manta ba mun kawo muku rahoto kan batun ɓacewar wani jirgin saman sojan saman Najeriya samfurin Alpha Jet (NAF475) a sararin samaniyar Maiduguri tun ranar Laraban nan da ta gabata.

Rundunar sojin saman Najeriya ta fitar da wata sanarwa dake cewa watakila jirgin nan nata da ya yi ɓatan dabo ranar Laraba a  jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar faɗuwa ya yi.

Kamar yadda gidan rediyon BBC Hausa ta ruwaito a shafin ta nuna internet cewa Wata sanarwa da Daraktan yaɗa labarai na rundunar sojin sama ya fitar Air Commodore Edward Gabkwet, a ranar Juma'a ta ce bayanan sirrin da suka tattara sun nuna cewa jirgin samfurin Alpha Jet (NAF475) yana ɗauke da mutum biyu.

Hakazalika ba'a san abin da ya haddasa hatsarin ba da kuma inda matuka jirgi biyu suke. Matuka jirgin su ne Flight Lieutenant John Abolarinwa da Flight Lieutenant Ebiakpo Chapele, in ji sanarwar.

BBC Hausa