Komitin Duba Wata a Najeriya sun sanar da cewa a Fara Sa idon ganin sabon watan Ramadan a yau Litinin


Ƴan Kwamitin duban wata na Najeriya sun umarci ƴan Najeriya da su fara duban jaririn watan azumin Ramadan daga ranar yau Litinin.

Shugaban Kwamitin, Farfesa Sambo Wali Wazirin Sokoto ya shaida wa BBC cewa, Litinin ce 29 ga watan Sha'aban kuma idan ba a gan shi ba da yamamcin Litinin, to za a ci gaba da duban watan zuwa ranar Talata.

Hakazalika Idan kuma ba a gan shi ba a ranar Talata, to kai tsaye ranar Laraba zata kasance 1 ga watan azumin Ramadana," in ji Waziri.

Farfesa Sambo ya ce babu yadda za a yi kwamitinsu ya saɓa da ka'idar duban wata da addinin musulunci ya gindaya saɓanin yadda wasu jama'a ke zato cewa ana yin shac

A cewarsa, kwamiti na amfani da Hadisin Manzon Allah (SAW) "ku yi azumi idan kun ga wata, ku ajiye idan kun ga wata - idan ba ku samu ganinsa ba kila saboda hadari to ku cika Talatin."

Ya yi watsi da zargin cewa suna tafiya tare da Saudiyya inda ya ce lokacin azumi kawai Saudiya ke duban wata saɓanin kwamitinsu da ko wane wata ke fita duban sabon wata.