Majalisar dokokin Najeriya ta bukaci Shugaba Buhari ya aiyyana dokan taɓaci a sha'anin tsaro


A yanzu haka dai Majalisar dokokin Najeriya ta bukaci gwamnati ta ayyana dokar ta-baci a kan tsaro tare da kara yawan sojoji da ƴan sanda, sakamakon tabarbarewa tsaro a ƴan kwanakin nan a yankunan ƙasar baki daya.

Majalisar wakilan ta na ganin cewa hakan ne zai sa a iya kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya.

An yi asarar rayukan jama`a a sassan ƙasar da dama, ga kuma fargabar da ake yi cewa mayakan na  boko-haram sun ƙwace iko a wasu yankunan jihar Neja, har sun kafa tutocinsu a ƴan kwanakin nan.

Shawarar majalisar wakilai ga Shugaban  ƙasa Muhammadu Buhari da cewa ya  ayyana dokar-ta-baci a harkar tsaro ta ƙasar, buƙata hakan  ya biyo bayan da mayakan Boko Haram ɗin da suka kwace wasu yankuna 42 a jihar Neja

Wannan na cikin ƙudurori 12 da ƴan majalisar suka zartar bayan awowi sama da uku suna tafka muhawara a zauren Majalisar.

Wasu ƴan Najeriya musamman arewacin kasar suna zargin gwamnatin tarayya da sakaci da rashin mai da hankali a kan harkokin tsaro wanda hakan shi ya haifar da ƙara faɗaɗar da ayyukan ta'addanci a sassan jihohin ƙasar.