Search Items

Makafi a Najeriya na korafi ba'a yi da su suna bukatar a basu Minista a cikin suWata ƙungiya da ke taimaka wa masu larurar nakasa a Najeriya ta yi alƙawarin cewa za ta raba sandunan jagora na Zamani ga masu fama da larurar gani  kimanin 10,000 a wasu sassan ƙasar nan.

Ƙungiyar mai suna 'Disability Resource Foundation of Nigeria' ta ce za ta raba sandunan jagora ne ga masu gani garara-garara da kuma marasa gani.

A cewar jagororin ƙungiyar ta bijiro da wannan tsarin ne da nufin rage musu  yawan haɗuran da sukan fuskanta a yayin zirga-zirga da kuma sanya su zama masu dogaro da kansu cikin al'umma.

Shugaban ƙungiyar Salisu Ibrahim ya shaida wa gidan rediyon BBC Hausa cewa ɗaya daga cikin abubuwan da suka ja hankalinsu wajen ƙaddamar da wannan shiri shi ne burinsu na tabbatar da cewa kowanne mai nakasar ido ya kasance yana da ƴancin fita ba tare da fargaba ba.

Kana ya faɗa cewa wasu za su yi mamakin hikimar raba sandunan, yana mai cewa yawancin sandunan da ake amfani da su ba waɗanɗa suka kamata a yi amfani da su ba ne a Najeriya.

Sannan ba su da ƙwarewa ko fahimtar yada ake amfani da sandar kuma wanda za a raba musu yanzu na musamman ce da aka ƙirƙira domin ta taimaka wa makafi ko waɗanɗa ba sa gani sosai wajen tafiya."

Hakazalika Salisu Ibrahim yana mai cewa basu bijiro da wannan shirin ba sai da suka yi bincike tare da gano manyan matsaloli kamar uku da masu larurar gani ke fama da shi.

Da farko sun fahimci cewa akasarin masau larurar basu iya amfani da sandunan zamani saboda tsadar su, sannan abu na biyu ba su da ilimin sanin yadda ake sarafata ko amfani da sandar, na uku kuma shi ne jin kunyar amfani da sandar."

Wadannan dalilai ne suka sanya aka ƙirƙiro shirin wayar da kawuna ta hanyar haɗa-kai da hukumomin kula da hanyoyi da ƙungiyoyin direbobi da malaman makarantu da ke koyar da amfani da sanduna da daliban makarantu da iyaye, sannan aka tsara littafin koyar da amfani da sanduna, in ji Salisu.

A cewarsa, sandunan kala biyu ne akwai na rukunin wanɗanda ba sa gani baki ɗaya, akwai kuma na masu gani garara-garara.

Sannan ya ce ana iya naɗe ta ko lanƙwasa sandar a jefa ta a cikin jaka ko aljihu duk lokacin da ba a bukatarta, sanduna ne na musamman da aka yi su domin daɗin tafiye-tafiye ga masu larurar gani

A karshe Salisu Ibrahim yayi korafi cewa ana yin gwamnatin Najeriya babu su wanda idan lokacin da zarar a buga gangan siyasa an san inda suke saboda ƙuri'u su.

Salisu ya bukaci a riƙa basu ministan harkokin su domin suma cikin su akwai masu ilimin da zasu iya mulkin wanda yace Hakan zai basu damar rage yawan masu barace-barace a tituna.

BBC Hausa