Manchester City Ta shirya tsaf kan cinikin Lionel Messi Daga BarcelonaJaridar Sun ta ruwaito cewa Manchester City na cike da burin ganin ta sayo dan wasan Barcelona Lionel  Messi, mai shekara 33, da kuma dan wasan Borussia Dortmund, Erling Braut Haaland mai shekara 20, dan kasar Norway, don ganin ta kawo su Etihad a bazara, 


Shi kuwa Paul Pogba ga alama burinsa na barin Manchester United zai iya cika nan kusa a bazaran nan, domin Juventus ta matsu domin ganin ta sake dawo da dan wasan na tsakiya dan kasar  Faransa, mai shekara 28. Har ma kungiyar ta Italiya na duba yuwuwar hadawa har da dan wasanta na gaba dan Argentina Paulo Dybala, mai shekara 27, ta bayar don ta karbo Pogban. Kamar yadda. 

Jaridar Manchester Evening News ce ta labarto cewa,Tottenham na ganin abu ne mai wuyar gaske ta rabu da tauraron dan wasanta na gaba, na Ingila Harry Kane, mai shekara 27. Kazalika ta ce ba ma za ta yi tunanin sayar wa wata kungiyar Premier shi ba, duk da yadda Manchester City da Manchester United ke nuna sha'awar sayensa. .

Ita kuwa kungiyar Bayern Munich tana son raba Tottenham din da dan wasanta na gaba ne Son Heung-min, mai shekara 28, kuma a shirye take ta bi sannu a hankali wajen ganin hakarta ta cimma ruwa ta samun dan wasan na Koriya ta Kudu, wanda sai a bazara mai zuwa 2023 yarjejeniyar zamansa a Tottenham zai kare, wanda kuma tuni kungiyar ta London ta kara yi masa sabon tayin kara lokacin zamansa a kungiyar. Football Insider ce ta ruwaito

BBC Hausa