Search Items

Manchester City tace bazata ci-gaba da zawarcin Lionel Messi ba


Ƙungiyar Manchester City na kokarin ganin ta cimma sabuwar yarjejeniya da 'yan wasan gaba na Ingila Phil Foden, mai shekara 20, da kuma Raheem Sterling, mai shekara 26, kafin karshen kakar da ake ciki, bayan da dan wasan ta na tsakiya, ɗan ƙasar Belgium Kevin de Bruyne, mai shekara 29, ya tsawaita kwantiragin zamansa har zuwa 2025.jaridar  Eurosport ce ta ruwaito hakan

A wata ruwayar kuma kamar yadda jaridar Telegraph ta ruwaito cewa an dakatar da tattaunawar Man City din da Sterling - wanda yake da sauran shekara biyu a wa'adinsa na zaman kungiyar har zuwa lokacin kasuwar saye da sayar da 'yan wasa ta bazara shigo

Haka kuma jagorar ta gasar Premier Manchester City ta ce ba za ta ci gaba da zawarcin Lionel Messi ba, mai shekara 33, dan kasar Argentina, har sai ya nuna cewa lalle yana son barin Barcelona. Kamar yadda jaridar Marca ta ruwaito.

BBC Hausa