Manchester United tana ɗari-ɗarin soma tattaunawa da Borussia Dortmund game da Erling Braut


Ƙungiyar Manchester United tana ɗari-ɗarin soma tattaunawa da Borussia Dortmund game da daukar ɗan wasan gaban Norway Erling Braut Haaland, mai shekara 20, saboda a bazarar da ta wuce Dortmund ta ki rage farashi kan Jadon Sancho.

Manchester Evening News ta ruwaito cewa Duk da rashin samun nasara a waccan tattaunawar, har yanzu Manchester United ba ta fitar da rai wajen daukar ɗan wasan gaban Ingila Sancho, mai shekara 21, a bazarar nan ba. 

Manyan kulop irin su Paris St-Germain, Real Madrid da Inter Milan suna sanya ido kan halin da Jesse Lingard yake ciki kafin buɗe kasuwar musayar ƴan kwallo ta bazara. Ɗan wasan na tsakiya mai shekara 28 ɗan kasar Ingila yana burge West Ham tun da ya je zaman aro a can daga Manchester United. 

Kulop ɗin Arsenal tana ci gaba da nuna sha'awa kan dan wasan gaban Celtic Odsonne Edouard kodayake tana fuskantar kalubale daga Leicester a yunkurin ɗaukar dan wasan na Faransa mai shekara 23 da ke buga gasar 'yan kasa da shekara 21.

BBC Hausa