Mayakan Boko Haram sun saka jihar Yobe a tsauri cewar Gwamnan Mai Mala Buni.Gwamnan jihar  Yobe Mai Mala Buni ya da  cewa suna cikin tsaka mai-wuya sakamakon hare-haren ƙungiyar Boko Haram da suka tada musu hankali tun  daga ranar Juma'ar makon jiya.

Gwamna Mai Mala ya ce sanin kowa ne halin da ake ciki a yankunan arewa maso gabashin Najeriya, sai dai hare-haren da suke gani a yanzu na tada hankula matuka kuma ya zama dole a ɗauki matakin tunkarar su.

A tattaunawarsa da BBC, gwamna ya ce da a baya komai yayi sauki amma a wannan lokaci abin ya tsananta matuka saboda ba a san dalilan mayakan ba, kuma zuwansu na wannan lokaci ya sha bamban da wanda aka saba gani a baya.

Waɗan nan Kalamai na  gwamna na zuwa ne a daidai lokacin da ake yaɗa cewa ba a ji komai daga gareshi ba tun da mayakan suka farwa garin suna kashe mutane da tilastawa daruruwan jama'a tserewa daga matsugunin su.