Muna tare da Ministan sadarwa Dr. Isa Ali Pantami cewar fadar Aso RockFadar gwamnatin Najeriya Aso Rock ta ce ta na tare da ministan sadarwa Isa Ali Pantami kan yanda ya ke bunkasa harkokin sadarwa da tattalin arziki.

Mai taimakawa shugaban Najeriya kan labaru Garba Shehu a wata sanarwa, ya ce gwamnatin ta gamsu da yanda ministan ya dage wajen rage farashin damar hawa yanar gizo ga talakawa.

Sanarwar martani ne ga wani kamfen din batunci ga ministan da wasu ke yadawa na nuna ya yi wasu kalamai a baya na mara baya ga tsaurin ra'ayi.

Garba Shehu ya ce lokacin da ministan ya yi irin wadannan kalaman ya na matashi a shekarun sa na 20, kuma ya janye ra'ayoyin, inda a badi zai cika shekara 50 a duniya.

Ra'ayin na fadar Aso Rock na nuna ba daidai ba ne yanda masu sukar ke yada lamura da su ka shude don ruguza darajar wani.


Yahaya Turba