Real Madrid ta shirya sayar da dan wasan tsakiya Martin Odegaard


Ƙungiyar Barcelona tana muradin daukar ɗan wasan gaba na Inter ɗan ƙasar Argentina Lautaro Martinez, mai shekara 23, a matsayin zabin da ya rage mata idan ba ta ɗauki ɗan wasan Haaland ba. Mujallar Sport ce ta ruwaito hakan.

Paris St-Germain za tana kila wa ƙalan  yiwuwar barin ɗan wasan Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 22, ya yi awon gaba a bazarar nan a yayin da ake samun turjiya game da sabunta kwangilarsa da ƙungiyar

Jaridar Metro ta labarai cewa Barcelona za ta kawo karshen zawarcin da take yi wa ɗan wasan Liverpool dan kasar Netherlands Georginio Wijnaldum, mai shekara 30, kuma maimakon hakan za ta bai wa ɗan wasan da ke tashe dan ƙasar Sifaniya mai shekara 18 Ilaix Moriba babban matsayi a kakar wasa mai zuwa.


Kocin Tottenham Jose Mourinho ya yi amannar cewa ɗan wasan Ingila Harry Kane, mai shekara 27, yana cike da farin ciki game da halin da yake ciki a kungiyar da ma kasarsa a yayin da ake hasashen zai bar kungiyar a bazara. (Standard)

Inter  zata cigaba da rike ɗan wasan Belgium Romelu Lukaku sai dai tayin da aka yi mata na £102m a kansa zai iya tilasta mata sayar da shi ɗan wasan mai shekara 27. Jaridar Corierre dello Sport ce ta ruwaito hakan.

Leicester City, Crystal Palace, AC Milan da kuma Sevilla suna son ɗaukar ɗan wasan Marseille ɗan ƙasar Faransa Florian Thauvin, mai shekara 28, a bazara.dake tafe

ESPN ta labarto cewa ƙungiyar Liverpool tana cikin tsaka mai wuya game da dan wasan gaban Masar Mohamed Salah yayin da wasu bayanai a cikin kungiyar suka tabbatar cewa dan wasan mai shekara 28 yana son barin kungiyar. 

Manchester United da Chelsea suna son daukar dan wasan Real Madrid dan kasar Sifaniya Lucas Vazquez, mai shekara 29. 

Chelsea na shirin ɗaukar ɗan wasan gaban Argentina Sergio Aguero, mai shekara 32, idan ya bar Manchester City a bazarar nan idan ta kasa daukar dan wasan gaban Norway Erling Haaland, mai shekara 20, daga Borussia Dortmund. (ESPN)

Real Madrid ta shirya sayar da dan wasan tsakiya Martin Odegaard domin ta samu kudin sayo Haaland. A halin da ake ciki Odegaard yana zaman aro a Arsenal kuma Gunners na son sayen dan wasan mai shekara 22 a mataki na dindindin.

BBC Hausa