Rundunar ƴan sandan jihar Kano tayi Nasarar ceto Yarinyar da aka kulle tsawon shekaru goma a ɗaki


Rundunar ƴan sandan jihar sun yi nasarar ceto wata yarinya a ranar Litinin mai suna Aisha Jubril wacce aka kulle a daki tsowon shekaru goma

BBC Hausa sun ruwaito a shafin su cewa Rundunar ƴan sandan Kano ta ce ta samu rahoto game da yarinyar dake kulle a ɗakin misalin ƙarfe 11 na safe, kuma nan take Kwamishinan ƴan sandan jihar ya bayar da umarnin a gaggauta ceto yarinyar.

Nan take rundunar ƴan sandan suka faɗa aikin ceton ƴan sandan sun ce sun samu yarinyar cikin wani mawuyacin hali na tsananin yunwa da kuma buƙatar kula da lafiyarta saboda irin yanayin da suka samu wurin da aka kulle ta ciki.

A Yanzu haka dai yarinyar ana aikin duba lafiyarta a asibitin Murtala dake garin Kano.

Sannan ƴan sandan kuma sun cafke mahaifiyarta mai shekara 35 da ake kira Rabi Mohammed yayin da mahaifinta kuma ya tsere Kamar yadda rundunar ƴan sandan ta Kano ta sanar

Kimanin shekara guda ke nan da samun irin wannan al'amari a Kano da sauran wasu jihohin arewacin Najeriya inda ake kullewa ko ɗaure yara ƙanana a ɗaki bisa don zuciya.

Sai dai kuma wannan karon an samu saɓanin yadda yawanci kishiyoyi ke aikata wannan aikin, amma wannan asalin iyayenta ne ake kyautata zaton sun kulle ta.

har yanzu dai ƴan sanda suna kan bincike da zarar bincike ya kammala za sun tabbatar da za su tura waɗanda ake zargi kotu domin fuskantar hukunci.

Shamsuddeen A. kano