Sergio Aguero ɗan ƙasar Argentina ya zama allurar cikin ruwa

Ƙungiyar Chelsea ce kan gaba a cikin kungiyoyin da ke da buƙatar daukar ɗan wasan ƙasar  Argentina Sergio Aguero  yayin da kwantiragin sa ta kare a Manchester City a bazara yayin da dan wasan mai shekara 32 yake son ci gaba da murza leda a gasar Firimiya Lig. (Mail)

Benfica ta kasar Portugal ita ce kungiya ta baya bayan nan da ke son daukar Agueron tun da rahoto ya bayyana ranar Litinin cewa zai bar Man City a karshen kakar wasa ta bana. (Record, via Mirror)

Sun ta ruwaito cewa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal da Independiente, kungiyar kasar Argentina inda Aguero ya soma sana'arsa ta kwallon kafa, sun bi sawun kungiyoyi dake zawarcin ɗan wasan irin su  Barcelona, Juventus da Paris St-Germain - da ke son ɗaukar ɗan wasan 

Liverpool za ta "fafata da" Barcelona a yunkurinta na daukar dan wasan Lyon da Netherlands mai shekara 27 Memphis Depay, wanda za a sanya a kasuwa a bazara. 

BBC Hausa