Shirin inganta tashar radiyo da talabijin na jihar Nasarawa ya fara gudanaGwamnatin jihar Nasarawa karkashin jagorancin injiniya Abdullahi A. Sule ta gudiri niyar inganta Babban tashar radiyo da talabijin na jihar (NBS) ta yadda tashar zata kasance daidai da takwarorin ta a faɗin ƙasar.

Shirin inganta tashar zai fara ne ta hanyar Samar da ingantattun na'urorin zamani a kowane fanni Ayyukan gidan rediyon da talabijin ɗin.

Hakazalika gwamnatin zata kowa kwararru da zasu karawa ma'aikatan sani ta fannin aiyukansu.

Wannan batun na zuwane a daidai lokacin da gwamnatin Injiniya Abdullahi Sule ke tunkarar shekaru biyu da kafuwa.

Al'umma jihar Nasarawa na tsokaci game da irin cigaba da aka samu cikin ɗan kankanin lokacin da yayi a kujerar mulkin jihar, musamman a aiyukan raya karkara da birane a faɗin jihar. 

Duk da irin matsalolin tsaro da ake fama dashi a ƙasa Jama'ar jihar Nasarawa sun yaba kwarai da irin jajircewar da gwamnatin jihar take yi wajen hanzarta dakile dukan wani nau'in rikici da ka Iya haifar da rashin zaman lafiya a jihar. 

Prince Abdullahi Attajiri baraden Keffi ya bayyana Gwamna Sule a matsayin guda ɗaya tilo da ke da cika alkawari kana ya mai da al'ummar jihar Nasarawa tsintsiya guda wajen hadin kai tsakanin juna.

Hakazalika ya bayyana shi da cewa mutum ne mai tausayi da sanin Yakamata, a ƙarshe ya yabawa al'ummar jihar Nasarawa da cewa mutane ne masu biyayya da don zaman lafiya.

Nasir H muhd