Shugaba Muhammadu Buhari ya buƙaci Amurka ta sauyawa hedikwatar rundunar sojin AFRICOM MatsuguniCikin wata sanarwa da mai magana da yaqin shugaban ƙasa Buhari ya gabatar Malam Garba Shehu ya sanar da manema labarai a ranar Talata, cewa Shugaban na Najeriya ya ce, akwai bukatar Amurka ta sauyawa hedikwatar rundunar sojin wanzar da zaman lafiya a Afirka ta AFRICOM matsuguni.

A cewar shugaba Buhari, yin hakan, zai mutukar taimakawa wajen daƙile yaduwar matsalolin tsaro a nahiyar  Afirka dama sauran yankin.

Wanda a yanzu haka hedikwatar ita AFRICOM yana can ne a babba birnin Stuttgart na kasar Jamus.

Hakazalika Shugaban na Najeriya ya mika wannan kokon bara ne ga Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken a ranar Talata, yayin wani taro da suka ta yanar gizo.

VOA