Search Items

Siyasa ta shigo cikin matsalar hare-haren da ke faruwa a kudancin Najeriya, In Ji masana harkokin tsaro


Masana harkokin tsaro ƙasa a Najeriya sun fara tsokaci game da yawaitar hare-haren da ƴan bindiga ke kai wa kan jami'an tsaro a wasu sassan jihohi a kudancin Najeriya a baya bayan nan.

Ranar Litinin ne hukumar kula da gyaran hali ta Najeriya ta ce ƴan bindiga sun kubutar da fursunoni 1,844 daga gidan yarin birnin Owerri na jihar Imo, bayan wasu ƴan lokuta  kaɗan bayan bankawa sashen binciken laifuka ta rundunar ƴan sandan jihar wuta.

Wannan al'amari na zuwa ne kwanaki kalilan, bayan sanarwar da rundunar yan sandan Najeriya ta ce yan kungiyar fafutukar kafa kasar Biafra wato IPOB ne ke kai wa jami'an tsaro hare hare a wasu jihohin kudancin Najeriyar.

Rundunar ƴan sandan ta kuma dora alhakin harin na ranar Litinin kan ƴan IPOB masu fafutukar kafa ƙasar Biafra.

Kwararran masanin harkokin tsaro a Najeriya Malam Kabiru Adamu daga kamfanin Baecon Consultancy, ya ce akwai alamun cewa siyasa ta shiga cikin wannan al'amari.

A cewarsa wasu ne ke yin amfani da wannan dama domin aiwatar da burinsu na tayar da yamutsi a Najeriya, alabashi sai su cimma manufofinsu Malam Kabir Adamu ya bayyana hakan ne yayin da yake tattaunawa da wakilin BBC.

Babban Sufeto Janar na ƴan Sandan Najeriya Mohammed Adamu ya ba da umarnin aikewa da wasu karin jami'an ƴan sandan kwantar da tarzoma zuwa Jihar Imo, inda aka ƙona ofishin ƴan sandan a safiyar Litinin 5 ga watan Afrilun 2021.

HaKazalika, rundunar ta ce binciken farko-farko da ta gudanar ya nuna cewa ƴan bindigar da suka kai harin mambobin ƙungiyar IPOB ne masu fafutikar ɓallewa daga Najeriya tare da kafa ƙasar Biafra.

BBC Hausa