Search Items

ƙungiyar Manchester zata karawa Juan Mata wa'adin kwangilan saƘungiyar ƙwallon ƙafa na Manchester United na shirin bai wa dan wasan tsakiya na Sifaniya Juan Mata, mai shekara 32, karin kwangilar shekara guda bayan ƙarewar wa'adin kwangila Sa a kulop din 

Shugaban da ke kula da kwallon kafa Sebastian Kehl ya amince da  cewa watakila Borussia Dortmund za ta kai wani mataki wanda ba za ta iya ci gaba da rike ɗan wasan kasar Norway mai shekara 20 Erling Haaland ba. 

Haaland ya sha gaban Lionel Messi ɗan wasan Barcelona dan kasar Argentina , mai shekara 33, a cikin jerin ƴan kwallon da Manchester City take da muradin ɗauka duk da yake kocinta Pep Guardiola ya ce kungiyar ba za ta maye gurbin Sergio Aguero, mai shekara 32 da wani ɗan wasaba

An yi amannar cewa Haaland yana son tafiya Real Madrid amma kungiyar ta Sifaniya ba za ta yi yunkurin daukarsa ba har sai shi da kansa ya nuna sha'awar hakan kana ya nuna cewa zai bar kulop dinsa Dortmund. 

BBC Hausa