Wasiƙa zuwa ga shuwagabannin kasashen Afirka da jama'ar Afirka baki ɗaya...


Ƙungiyar kare hakkin bil'adama kuwa...?
Dr. Safwan Salim. 

Hausawa su kan ce ruwa chokali guda ya ishi mai hankali wanka. Ya kamata shuwagabannin kasashen Afirka su daina zama da Kai su tsaya da ƙafafuwan su, su fuskanci matsalolin su.

Idan muna tare da mai karatu da kanka zaka fahimci cewa akwai lauje cikin naɗi a ƙasar Libiya turawan yammacin duniya sun bada gudunmawa wajen yaƙar marigayi col. Gaddafi.

Bayan mutuwarsa aka kafa gwamnatin da suka daure wa gindi a matsayin gwamnatin da aka kafa da sunan demokradiyyar achan sunan su masu adawa da gwamnatin ƴan ta'adda aikin da suka saka gwamnatin Libya shine kwace makamai Daga hannun farar hula.

Kungiyar Boko Haram Su shafe shekaru suna bankawa kasuwani, Ma'aikata, makarantu. Bama-bamai amma babu wata gudunmawar wanda da ni da ku zamu ce hukumar kare hakkin bil'adama ta duniya ta bayar domin murkushe su.

Shuwagabannin mu ma na tsoron kada su dauki matakin murkushe su a ƙungiyar kare hakkin ƴan ta'adda su yanke musu irin hukuncin da aka yanke wa shugaban ƙasa Saddam Hussein.

Ƙasar Çhadi dake fama da matsanancin rashin tsaro da barazanar ƙungiyar ƴan ta'adda Amma wasu marasa kishin kansu sun haɗa zanga zangar kin amincewa da mulkin soja gwamnati ta ɗauki matakin daƙile yunƙurin su.

Kwatsam sai ga kungiyoyin masu kiran kansu sune masu kare hakkin bil'adama suna faɗin sunyi Allah wadai da matakin gwamnati saboda an kashe mutane 6 kuma an kame da yawan masu zanga-zangar Bayan idan aka barsu kamar haka zasu canza suna gobe zuwa wani kalar finawa ƙasar da sunan yancin.

Libya.Sudan, Somalia,dama kasar Iraki sun ishe ku Misali in kunne ya ji

A Karshe shawara ta shuwagabannin kasashen Afirka ku lura da jama'ar ku da hakkin su ƙungiyoyin ta'addanci sun buwayi ƙasashen ku su yaki ku yake su kafin kafa wani shashanci wai ita Dimokradiyya.

Nasir H. Muhammad