'Yan jami'iyar adawa ta PDP suna gani akwai yiwuwar mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbanjo ka iya taka rawar gani fiye da Shugaba Buhari


Wasu masu sharhi na ganin rashin baiwa mataimakin shugaban kasa daman rike kasar yayin da shugaban ya tafi kasar waje don duba lafiyar sa a Ingila,hakan  ka iya shafar dangantakarsu.

'Yan jami'iyar adawa  ta PDP suna gani akwai yiwuwar mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbanjo ka iya taka rawar gani fiye da Shugaba Buhari  yayin da aka bar masa ragamar gudanar da mulkin kasar ne ya sa ba a ba shi rikon kasar na wucin gadi a lokacin da shugaban kasar zai je ganin likitocinsa a Ingilar ba.

A hirarsa da Muryar Amurka tayi da  Malam Garba Shehu mai magana da yawun Shugaban kasar ya ambato dokar Najeriya da ke cewa dole shugaban kasa ya mika ragamar mulki ga mataimakinsa idan zai bar kasar sama da kwanaki 21, amma ya ce shugaba Buhari ba ma zai kai kwanaki 20 a wannan ziyarar duban lafiyarsa ba  don haka baya ganin akwai wata matsala game da hakan.

hakazalika ya kara da cewa idan shugaban ya yi abin da ya sabawa doka ko majalisar dokoki za ta iya mika ragamar mulkin ga mataimakinsa.

Sai dai akwai masu ganin cewa rashin baiwa mataimakin shugaban kasa daman rike kasar yayin da shugaban ke duban lafiyarsa a Ingila ka iya shafar dangantakar shugaban da mataimakinsa, batun da Malam Garba Shehu musunta.

Ya ce kyakkyawar dangantaka dake tsakanin shugaban kasa  da mataimakinsa Osinbanjo tana nan daram kuma wannan ba zai bata tsakanin su ba saboda suna aiki tare da yarda da aminci dan haka ya ce bai ga wani dalilin da zai sa mutane su yita fargaba ba farfaganda ce kawai iri na yan adawar gwamnati.

Malam Shehu ya yi fatali da abin da wasu ke tunani cewa kila mataimakin shugaban na da wata gazawa ne shi ya sa shugaban kasa bai bar masa riko ba.

Ya kara da cewa  babu wani takamaiman aiki na musamman  da doka ta ware wa mataimakin shugaban kasa sai wasu ‘yan kalilan da shugaban zai umarce shi da ya yi kuma babu wanda ya san abin da suka yi tsakaninsu kafin tafiyar tasa dan haka bai yiwuwa a ce mataimakin nadawata gazawa.

A bangaren ‘yan adawa suna gani an shirya ne domin tabbatar da ganin cewa Yemi Osinbanjo bai sake rike mulki na wucin gadi ba kamar yadda aka yi a baya.

source VOA Hausa