Yan kungiyar Biafra Sun kashe Hausawa 12-Alhaji Amadu AliRahotanni daga jihar Imo a Kudu maso gabashin Najeriya sun bayyana cewa mutum uku sun hallaka bayan wani hari da ake zargin Kungiyar mayakan Biafra ce ta kai wa al'ummar Hausawa da ke  zaune a yankin Orlu dake  jihar Imo.

Wannan  al'amarin dai ya jefa al'ummar Hausawan da ke yankin kudancin Njeria a cikin zaman zulumi.

A cewar wani  Bahaushe dan kasuwa mazaunin yankin na Orlu, Alhaji Amadu Ali, tun daga watan Agustan bara zuwa yanzu, kungiyar ta Biafra ta halaka Hausawa 12 baya ga asarar dukiya ta kusan naira miliyan 42 da suka tafka.

Cikin jawabin sa yake cewa Mu dai mun tashi kawai ranar Laraba, wani mai nama, yana tafiya ya dawo da wuri kawai ya haɗu da waɗan nan mutanen suka buɗe masa wuta, abin da suka sakar masa harsashi na AK47,nan take  ya mutu", in ji Alhaji Ahmadu Ali.

Alhaji Ahmadu Ali.Ya fadawa wakilin  BBC cewa lamarin ba mai naman kadai ya shafa ba har da wani ɗan sarkin gari  shima sun halaka shi.

Dan kasuwar ya ce ba zai iya bayyana wani dalili da ya sa yan Biafran suke kai musu hari ba "don bamu da fada da kowa, kuma  babu wanda mu ka tsokana 

"Tun daga ranar da aka yi (rikicin) Endsars suka fara kashe mutanenmu ɗaya bayan ɗaya", in ji Alhaji Amadu Ali.

Ya ce kawo yanzu, yan Biafran ba su fara bi gida-gida ba amma suna kai hari ne kan masana'antun Hausawa inda suke harbe su da dai-daya.

Ya yi ikirarin cewa hukuma tana sane da abin da ke faruwa a jihar saboda "ƴan sanda su suka bamu motar da muka dauki gawar mutum uku muka bizne kuma sai da kwamishinan ƴan sanda ya yi magana a bamu gawar sannan aka bamu".

source BBC Hausa