Yawan bazuwar Makamai yayi sanadiyyar mutuwar mutum aƙalla 80,000. A Najeriya


BBC Hausa ta ruwaito tsohon shugaban Najeriya Janar Abdulsalami Abubakar ya alakanta karuwar tashe-tashen hankula a ƙasa da yawaitar makamai da aka samu a hannun ɗai-ɗaikun mutane, inda ya ce akwai a ƙalla makamai miliyan shida da ke yawo a hannun mutane ba bisa ƙa'ida ba.

Tsohon shugaban wanda kuma shi ne shugaban kwamitin zaman lafiya na ƙasar ya bayyana hakan ne yayain wani taron tattaunawa tsakanin masu ruwa da tsaki da ya gudana a ranar Laraba a Abuja.

A cewarsa, shigowar bazuwar makaman wanda ya haifar da matsalar tsaron a Najeriya ya yi sanadiyyar mutuwar mutum aƙalla 80,000.

Manyan mutane da dama sun halarci Wannan gagarumin  taron wadanda suka hada da shugaban cocin katolika na Sokoto, Matthew Kukah da Sarkin Musulmai Sultan Sa'ad Abubakar III; da shugaban kungiyar gwamnonin arewa Simon Lalong da babban attajiri nan Aliko Dangote da sauran mambobin kwamitin.

Hakazalika ya ce, "Bazuwar muggan makamai a baki ɗayan Najeriya abin damuwa ne. An yi ƙiyasin cewa akwai fiye da makamai miliyan shida da suka yaɗu a ƙasar nan.

Ya kara da cewa rikici na matsalar tsaro ya hallaka mutum 80,000 sannan ta raba kusan wasu miliyan uku da muhallansu," in ji tsohon shugaban kasan Abdulsalami.

Shi ma tsohon shugaban Najeriya Janar Yakubu Gowon ya shawarci 'yan Najeriya cewa a ajiye maganar addini da kabilanci a san cewa matsalar Najeriya ta duka 'yan kasar ce.

BBC Hausa