Za'a binne aƙalla Mutane 50 a kauyen Zamfara wanda ƴan bindiga suka kashe

A yau ne za a sake yin jana'izar ƙarin wasu mutane da ƴan bindiga suka kashe bayan wani mummunan artabun da ya zama sanadin mutuwar gomman mutane a jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya.

Wani wanda abin ya faru gaban su ya faɗa wa BBC cewa ya zuwa yammacin Laraba, sun ƙirga mutum 51 da aka kashe daga ƙauyukan gundumar Magami daban-daban.

Ƴan bindigan sun auka wa mutane ne lokacin da suka yi yunƙurin kai ɗauki ga mutanen ƴar Doka, waɗanda wasu bayanai ke cewa sun koma gida daga gudun hijira, kwana ɗaya rak  kafin wannan ƙazamin hari da aka kai musu.

Rahotanni sun ce har zuwa daren jiya Laraba mutane na ci gaba da tsere wa ƙauyukan yankin zuwa gudun hijira a Magami mai nisan kimanin kilomita 18.

Shaidu sun ce cikin mutanen da aka kashe akwai aƙalla mutum 20 daga ƙauyen Ruwan Dawa, sai goma na Kangon Fari Mana, shida daga Madaba, Arziƙin Ɗa ma mutum shida, Mai Kogo da Mai Aya-aya da Mai Rairai kowanne mutum biyu da Gidan Maza da Kunkelai mutum ɗai-ɗai.

Wannan shaida daga Kangon Fari Mana ya ce ƴan bindigan sun shafe kimanin awa bakwai suna harbe-harbe a cikin ƙauyukan.