An gano gawar Iniobong Matar da ta ɓace yayin neman aiki a Akwai Ibom.

Karshe an gano cewa wata mata mai suna Iniobong Umuoren da ta bace a tafiya zantawar neman aiki a jihar Akwa Ibom kashe ta a ka yi a ka bunne ta a wani karamin kabari.

Iniobong wacce ta kammala karatu a jami'ar Uyo ta fita neman aiki ne a wajen babban birnin jihar Uyo inda matashin da ya yi ma ta alkawarin aikin mai suna Uduak Akpan ya yaudare ta zuwa gidan mahaifin sa inda ya yi ma ta fyade daga nan ya kashe ta kuma ya bunne ta a haranar gidan.

Uduak Akpan mai shekaru 20 ya saba yi wa ma ta fyade a baya ta hanyar irin wannan yaudara.

An cafke Akpan kuma za a gurfanar da shi gaban kotu don amsa laifukan fyade da kashe rai ba da hakkin shari'a ba.

Rundunar 'yan sanda a jihar ta yabawa ma'abota yanar gizo don ya da su ka yayata kamfaen na neman inda Umuoren ta shiga bayan an rasa inda ta ke yayin da ta fita neman aiki.

Hakazalika a jihar ta Akwai Ibom a bankawa offishin Hukumar zaben Najeriya INEC ta ce an bankawa ofishin ta da ke karamar hukumar Essien Udim a jihar Akwa Ibom wuta.

Kwamishinan labaru na hukumar Festus Okoye ya baiyana haka a wata sanarwa.

INEC ta ce mai gadin ofishin ya samu ya arce daga ofishin ba tare da samun rauni ba.

Kazalika sanarwar ta zaiyana cewa wasu ne da ba a san ko su waye ba sy ka kau harin.

Motoci, akwatunan zabe da sauran takardu sun kone kurmus a ofishin.


Yahaya Turba