An kashe Ƴan sanda a wani harin ta'addanci a jihar Akwai Ibom
Rahoto daga jihar Akwa Ibom dake a kudancin Najeriya na baiyana rasa ran jami'an ƴan sanda biyu a sanadiyyar harin da ƴan bindiga su ka kai mu su.

Harin ya auku ne a wani ofishin ƴan sandan da ke karamar hukumar Ikono.

Baya ga kisan gilla ga ƴan sandan biyu wata jami'ar ƴan sanda ma ta samu raunuka inda a ka cinnawa motoci 5 da ke harabar ofishin wuta.

Ana zargi ƴan neman raba Najeriya IPOB ne a yankin su ka kai wannan harin kamar yanda su ke ƙara matsa lamba don tada fitina a yankin kudu maso kudu da kuma yankin su na asali kudu maso gabar.

Tuni dai hukumomi da jami'an tsaro suka sunkuya aiki tuƙuru don gano masu ruwa da tsaki cikin ta da fitinu a yankunan da ke kudancin Najeriya.

Yahaya Turba