Ana yiwa Gwamnatin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zagon ƙasa don kifar da ita


Fadar Aso Rock ta yi zargin cewa wasu tsoffin shugabannin siyasa da malaman addini suna yin markashiyar da za ta kai ga kifar da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar Femi Adesina ya aike wa manema labarai ta ce mutanen suna son kawo yamutsi a kasar ne sanna su yi amfani da damar wajen kifar da gwamnatin.

A Ranar Lahadi Hukumar tsaron farin kaya ta (DSS), ta jawo hankali game da muguwar aniyar wasu da ke son hargitsa gwamnati da dorewar kasar.Wasu malaman addini da tsoffin masu rike da mukaman siyasa da da ba sa kishi ne suke gaba-gaba, kuma manufarsu ita ce daga karshe kasar ta fada cikin rikici, wanda zai tilasta sauya shugabancin zuwa wanda ba na dimokradiyya ba," in ji Mr Adesina.

Ya kara da cewa wasu hujjoji masu kwari sun nuna cewa wadannan mutanen suna daukar nauyin shugabannin wasu kabilu da 'yan siyasa a duk fadin kasar, bisa niyyar gudanar da tarukan da za su yi Allah-wadai da shugaban kasa, lamarin da zai kara jefa kasar cikin yamutsi.

A cewarsa, wasu mutane sun rika gudanar da wasu abubuwa da zummar share hanya wajen jefa kasar cikin hargitsi.Kakakin na Shugaba Buhari ya ce manufar mutanen ita ce cimma burinsu wanda suka gaza samu a lokacin zaben 2019.

Hakazalika ya kara da cewa 'yan Najeriya sun zabi a yi musu mulki na dimokradiyya kuma ba za su amince da wani mulki ba idan ba na dimokradiyyar ba.

Source: BBC Hausa