Manchaster City ba guri zaman kowanne irin ɗan wasa bane cewar GuardiolaKocin ƙungiyar Manchester City Pep Guardiola ya ce, kungiyar ba wurin zuwan duk wani ɗan wasa ba ne da ba ya son a riƙa sauya masa wurin da yake taka leda a fili ba. Jaridar Manchester Evening News ce ta ruwaito hakkan.

Tashar Sky Sports ta Nuno tsohon ɗan wasan tsakiya na Manchester United Roy Keane yana cewa yana ganin in dai har kungiyar na son ta kalubalanci gogayya da abokkiyar hamayyarta Manchester City a kaka mai zuwa to ya kamata ta dauki dan wasan gaba na Tottenham Harry Kane, mai shekara 27 da abokin wasansa a tawagar Ingila Jack Grealish mai shekara 25 da ke Aston Villa.Jaridar Karva ce ta ruwaito cewa Darektan wasanni na Paris St-Germain Leonardo na nuna shakku idan har ɗan wasan gaba na Brazil Neymar, mai shekara 29, zai sabunta yarjejeniyar sa ta ci gaba da zamansa a kungiyar ta Faransa. 

BBC Hausa