Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen jihar Kaduna sun damƙe mutane hudu da suka sace ɗan maƙwabtan su


Rahotannin na ƙara fitowa fili dangane da kisan wani yaro ɗan kimanin shekaru biyar, da wasu mutum hudu suka yi a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya cikin wannan mako.

Wani ƙanen mahaifin yaron mai suna Sanusi Jibo Magayaƙi, ya shaida wa wakilin BBC cewa tun farko an nemi Muhammadu sama ko kasa an rasa shi tun a ranar Asabar din da ta wuce, amma daga bisani iyayensa sun samu labarin cewa an gan shi a jihar Kano tare da wani mai suna Galadima.

Ya ce wani ɗan unguwa ne ya ga Galadima wanda ɗan unguwar su Muhammadun ne a tashar mota a Kano, lamarin da ya sa ya ɗauki hotonsa ya aika wa mahaifinsa, sai dai kafin a tura jami'an tsaro sai aka neme su aka rasa Galadima ya ranta a na kare.

A na cikin haka nan ne wadanda suka yi garkuwa da shi sai suka bugo waya, cewa lallai yaro na hannunsu kuma sai an ba su kuɗi za su sake shi, inda suka nemi Naira miiyan 50, kafin daga bisani aka yi ta gangarowa kasa har aka sakko zuwa Naira miliyan biyar", in ji shi.

Jibo ya baiyana cewa an kai musu kuɗi inda suka nemi a kai, wato kusa da gadar sama dake  Kawo a garin Kaduna, amma sai daga baya aka ki ba su yaronsu har tsawon kwana guda.

Magayaƙi ya bayyana wa BBC Hausa cewa mutanen sun yanke shawarar kashe Muhammadu ne saboda zai iya fadar cewa su ne suka sace shi, tun da dama ya sansu a matsayin makwabtan gidansu.

A cewarsa "An kama Galadima a Kaduna, inda kuma ya shaida wa jami'an tsaro cewa Muhammadu yana Kano, lamarin da ya sa aka tafi da shi da rakiyar jami'an tsaro domin gano gawarsa.

Ko da aka je Kano sai ya fara yi musu wasa da hankali, sai da aka kai shi wajen kwamishinan yan sandan jihar Kano aka yi masa barazana da hukunci mai tsanani, sai ya fadi cewa su ne suka kashe Muhammadu."

Hakazalika ya tabbatar da gaskiyar rahotannin cewa Galadima wanda shi aka fara kamawa yana da hannu a wannan al'amari tsohon sojan Najeriya ne, sai dai an kore shi daga aiki a shekarun baya.

A halin da ake ciki dai a cewarsa an kama mutane hudu da ake zargi da hannu a wannan al'amari, da suka hadar da Nazifi, wanda shi ne ya fara daukar Muhammadu ya mika wa Galadima, da kuma wata mata da aka ajiye yaron a gidanta lokacin da aka boye shi a jihar Kano, da kuma Galadima da wani mai suna Umar, wanda shi ne ya rika yin waya da iyayen yaron a lokacin da ake tsare da Muhammadu.

Source BBC Hausa