"Dara ta ci gida: Ƴan fashi sun kashe Auwalu Daudawa da yayi tubar muzuru a daren jiya.


Gwamnatin jihar Zamfara  ta sanar da cewa an kashe Auwalu Daudawa, kasurgumin dan fashin dajin nan da ya yi tuban mazuru, ya kasance cikin ƴan bindigan da ke da hannu wajen sace daliban sakandaren Kankara.

Kwamishinan Tsaron jihar, Abubakar Muhammad Dauran, ya shaida wa  gidan rediyon BBC Hausa cewa an kashe shugaban ƴan fashin dajin ne sakamakon rikicin da ya barke tsakaninsa da kungiyoyin ƴan fashin da ke hamayya da shi.

A cewar Muhammad Dauran an kashe ɗan  fashin ne tare da wasu mabiyansa a yayin fafatawar da sukayi da juna a daren juma'an nan da ta gabata.

A labarin da  muka samu cewa an kashe Auwalun Daudawa...har ya dauki shanun wasu, kuma su ma wadannan ƴan fashi da ke yankin sun dauki alkawarin ajiye makamansu. To, a wannan ne hadari ya same shi aka kashe shi. Labarin da yake zuwo mana ke nan," in ji Kwamishina Dauran.

Har I zuwa lokacin kammala wannan rahoto Muhammad Dauran yace basu samu ganin gawar ɗan fashin dajin ba.

Sai dai Dauran ya tabbatar da cewa akwai wadanda suka ga gawar dan fashin kuma ba shi kaɗai aka kashe ba, duk da cewa  shi ma ya kashe wasu.

Amma hukumar zata faɗaɗa bincike don tabbatar da sahihancin al'amarin.

BBC Hausa