Jam'iyun APC da PDP na cece ku ce kan haramta shafin twitter a NajeriyaMujalar BBC Hausa ta wallafo cewa Babbar jam`iyyar adawa a Najeriya wato PDP ta buƙaci ƙasashen duniya su sanya wa Shugaba Muhammadu Buhari da ministocinsa da kuma shugabannin jam`iyyar APC takunkumin tafiya zuwa ƙasashen ƙetare.

Ta ce matakin na da alaƙa da dakatarwar da gwamnatin Najeriya ta yi wa shafin sada zumunta na Tuwita a Najeriya.

PDP ta ce hakan yunƙuri ne na tauye `yancin faɗar albarkacin baki kuma a bayanin da ya yi a Turanci , Mista Kola Ologbondiyan, Sakataren yada labaran jam'iyyar ya ce "PDP na kira ga Amurka da Burtaniya da Canada da Saudiyya da sauran ƙasashen duniya da su gaggauta haramta izinin shiga ƙasashensu ga Shugaba Buhari da daukacin yan majalisar da ke da hannu wajen tauye yancin fadar albarkacin baki a Najeriya."

"PDP ta dogara ne ga hujjar da take da ita cewa Shugaba Buhari ya saɓawa kudirin Majalisar Dinkin Duniya a kan hakkin bil adama sakamakon matakin da ya dauka na haramta amfani da Tuwita a Najeriya." in ji Kola Ologbondiyan.

Sai dai Mallam Salisu Na'inna Danbatta, Daraktan yada labaran jam`iyyar APC mai mulki ya ce PDP ta jahilci harkar diflomasiyya.

"Hulda tsakanin kasa da kasa musamman babbar ƙasa kamar Najeriya wadda take da martaba da daraja a duniya kasan daga jin wannan magana ta PDP, za ka iya daukar cewa su jahilai ne kan al'amarin diflomasiyya,"

"Watakila suna so su zubar da martaba da kimar ƙasarsu wadda wata rana suke so su rabi mulkinta, wanda zai yi wannan yana da mishkila." in ji Daraktan yada labaran APC.

Ya ce kiran da PDPn ta yi ba shi da wani tasiri a kunnuwan ƙasashen saboda ƙasashen duniya suna da bukatunsu - "da wuya ka ga wata kasa a duniyar nan ta yi wasa da martabar Najeriya yadda za ta tsinkata".

Tun farko PDP ta ce haramta amfani da Tuwita zai janyo babban koma-baya a kasar abin da APC ta ce dakatarwar ta kara farin jinin Shugaba Buhari da kuma jam'iyyar APC a zukatan yan kasar tare da samun hadin kansu tun da Najeriyar ta nuna kasa ce mai cikakken yanci da ba za ta bari a yi mata hawan kawara ba.

BBC Hausa